Rashin Tsaro Ba Zai Hanamu Cigaba Da Harkoki Ba – Fadar Shugaban Kasa

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Fadar shugaban kasa ta kara jaddada cewa Najeriya har yanzu ita ce kasar da ta fi dacewa masu zuba hannayen jari a Afrika su yi tururuwar zuwa duk da kalubalen tsaro.

Femi Adesina, mai bada shawara ta musamman ga shugaban kasa a fannin yada labarai, ya sanar da hakan a wata tattaunawa da yayi da gidan Talabijin na Channels.

Kamar yadda yace, duk da kalubalen tsaron da ke addabar Najeriya wanda ya hada da Boko Haram, rikicin makiyaya da garkuwa da mutane, ba zai hana masu zuba hannayen jari daga kasashen duniya zuwa Najeriya yin kasuwanci ba.

Ya kara da cewa, masu saka hannayen jari sun san cewa a lokutan da kalubale yayi yawa ne ake samun damammaki, wannan zai karfafa su kuma ko kaɗan ba zai shafi gudanar da harkokin Shugaban ƙasa ba.

Adesina ya yi jawabi kan alfanun ziyarar aikin kwana hudu da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai Dubai, Hadaddiya Daular Larabawa inda ya halarci taron Expo 2020.

A yayin karin jawabi, Adesina ya ce shugaban kasan ya yi daidai inda yace Najeriya ce wurin da ya fi dacewa da masu zuba hannayen jari a Afrika.

A yayin da aka tambaye shi ko masu zuba hannayen jari za su iya zuwa su narka kudadensu a Najeriya duk da kalubalen tsaro, Adesina yace:

“Idan har ka na tunani kamar mai zuba hannun jari, za ka gane cewa gara ka zuba kudin ka a inda babu zaman lafiya. Saboda idan ka zuba kudin ka a wurin da ke da matsala, za ka samu alheri mai yawa saboda matsalar bayan komai ya lafa.”

Labarai Makamanta