Rashin Tarbiyya Ne Silar Matsalar Tsaro – Sarkin Musulmi

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Dr Muhammad Sa’ad Abubakar III, yace rashin kular iyaye yana cikin dalilan da yasa ake samun matsaloli acikin al’umma, wanda ya yi sanadin taɓarɓarewar tsaro har muka tsinci kanmu inda muke ciki a yanzu.

Sarkin Musulmi yayi wannan jawabi ne a ranar 9 ga watan Nuwamba, 2021, a yayin wani babban taro na kaddamar littafi kan ilimi da ya gudana a birnin tarayya Abuja.

Mai alfarma Sarkin Musulmi yana ganin akwai sakacin iyaye wajen kulawa da yaransu da kuma rashin samun kyakkyawar dangataka wajen tabarbarewar al’amura.

Muhammad Sa’ad Abubakar III ya yi wannan bayani ne a birnin Abuja a ranar Litinin a wajen bikin kaddamar da littafi da Dr. Yakubu Gambo ya rubuta kan muhimmacin ilimi a matakin farko.

Dakta Yakubu Gambo ya rubuta littafi mai suna ‘Evolution of Day Secondary School in Nigeria’ wanda ya yi bayani a kan kaimin makarantun je ka-ka dawo a Najeriya.

Mai martaba Sarkin Wase, Dr. Mohammed Sambo Haruna ya wakilci Sarkin Musulmi a wajen taron, inda ya nemi iyaye su maida hankali wajen bada tarbiyya. “A madadin shugabanninmu, ina kira ga dukkaninmu (iyaye), mu koma muyi abin da ya dace.

Akwai bukatar mu ba ‘ya ‘yanmu kulawar da suke bukata.” “Wadansu daga cikin matsalolin da muke fuskanta a yau, suna aukuwa ne saboda (iyaye) ba mu da alaka da ‘ya ‘yan na mu.”

Labarai Makamanta