Rashin Tarbiyya Ce Ke Haifar Da Cikin Shege – Kwamandan Hisbah

Babban kwamandan hisbah na jihar Kano Dr Ustaz Harun Muhammad Sani ibn Sina yayin da yake duba ayyukan da suke shigowa hukumar ta Hisbah ya ga karuwar abubuwa guda biyu, wato yawan batan yara da haihuwar ‘ya’ya ba tare da aure ba.

Don haka ya ja hankalin iyaye akan bace-bacen yara da yake kara yawaita a yanzu. Inda Babban kwamandan Hisbah ya ce ya kamata iyaye su sani cewa yara da Allah yake bawa iyaye wata babar baiwa ce wadda wasu ba su samu ba. To kai da Allah ya baiwa ya kamata ka alkinta.

Haka zalika Dr ibn Sina ya akara jan kunnen iyayen yara da su kara kula sosai da shige da ficen ‘ya’yansu, domin idan aka samu yawaitar irin wannan matsalolin za a samu lalacewar tarbiya da lalacewar arziki daga nan kuma, al’umma za ta lalace sai kuma fushin Allah ya tabbata akan wannan al’ummar.

Labarai Makamanta