Rashin Makamai: Sojoji Sun Gudanar Da Zanga-Zanga

Dakarun Sojojin rundunar Operation Lafiya Dole sun gudanar da wata zazzafar zanga-zanga sakamakon turasu fagen yaki da ‘yan ta’addan Boko Haram ba tare da isassun makamai ba.

A cewar majiyoyi daga barikin Maimalari dake birnin Maiduguri fadar gwamnatin Jihar Borno Sojojin sun mamaye hedkwatar Operation Lafiya Dole ne a daren Alhamis suna harbin bindiga sama.

Dakarun Sojin sun bayyana cewa suna zanga-zanga ne sakamakon rashin biyansu alawus da kuma rashin isassun makaman yaki.

A jawabin wasu daga cikin sojojin da suka bukaci a sakaye sunayensu, sun bayyana yadda yan ta’addan Boko Haram suka hallaka Sojoji a harin Marte saboda makaman yan ta’addan sun fi nasu.

Gidan talabijin na Channels ya bayyana cewa kakakin rundunar Operation Lafiya Dole, Kanal Isa Ado, ya tabbatar da labarin.

Wannan zanga-zanga ta Soji ta biyo bayan fallasan da mai bada shawara kan harkokin tsaro Babagana Munguno yayi cewa an nemi kudin makamai an rasa karkashin tsoffin hafsoshin tsaro.

Mai bada shawara kan lamarin tsaro, Babagana Monguno, ya yi zargin cewa wasu kudaden da aka ba tsoffin hafsoshin tsaro domin sayan makamai sun yi batan dabo.

A cewar Monguno, an bada kudaden ne domin sayen makamai don karfafa yakin yan ta’addan Boko Haram. Monguno ya yi wannan fallasa ne a hirar da yayi da BBC Hausa ranar Juma’a, 12 ga Maris.

Amma mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu, ya bayyana cewa ba zai yiwu a ci kudin makamai karkashin shugaba Muhammadu Buhari ba.Shehu ya bayyana hakan a shirin Politics Today na ChannelsTV ranar Juma’a inda yace kudi $1billion da aka saki a 2018 don sayen makamai, an yi amfani da su.

Labarai Makamanta