Hukumar kula da gidajen yaɗa labarai ta ƙasa BON ta bayyana karancin wutar lantarki da tsadar man dizel a matsayin wani tarnaƙi dake kassara ayyukan gidajen yaɗa labarai a Najeriya.
A gefe guda kuma Hukumar ta koka akan yadda taurin bashi da kin biyan bashin gaba ɗaya daga masu kawo tallace- tallace a matsayin wata babbar barazana ga rayuwar kafafen yaɗa labarai a faɗin ƙasar.
Da yake Jawabi akan gudummawar da sashin ya bayar a cigaban ƙasa a shekarar da ta gabata ta 2022, babban sakataren Hukumar Dr Yemisi Bamgbose yace gwamnatin tarayya da Jihohi da sauran masu kafafen yaɗa labarai su sanya himma wajen tabbatar da samun kudaden shiga da za su tallafi gidajen yaɗa labarai mallakin su domin cigaban dimukuraɗiyya.
“Gwamnatin ta samar da kuɗaɗen da suka dace ga hukumar NBC domin ba ta damar samar da shirye-shirye waɗanda za su taimakawa masu ruwa da tsaki da sauran jama’a gaba ɗaya.
“Shekarar da ta gabata shekara ce da hukumar samar da wutar lantarki ta samu gazawa da manyan ƙalubale wajen samar da wutar lantarki amma hakan bai hana mika dogayen bill ba da sunan tana bin bashi ga kafafen yaɗa labarai.
“Bamgbose wanda ya buƙaci a mayar da hankali sosai wajen inganta ayyukan gidajen rediyo da talabijin masu zaman kansu ta hanyar yin haɗaka dasu wanda zai basu damar amfani daga kuɗaɗen tallace-tallace.
Babban Sakataren ya kuma bada tabbacin cewa masu gidajen yaɗa labarai za su cigaba da gudanar da ayyukan su bisa gaskiya kamar yadda kundin tsarin mulki ya basu ba tare da tsoro ko fargaba ba, duk da kalubalen da suke fuskanta musanman na rashin wutar lantarki.
You must log in to post a comment.