Rashin Lafiya: Buhari Ya Yi Addu’ar Samun Lafiya Ga Sheikh Dahiru Bauchi

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya aike sakon gaisuwa ga Sheikh Mohammed Dahiru Bauchi bisa labarin rashin lafiyarsa da ya samu. Buhari ya aike sakon ne ta bakin Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ranar Alhamis, 8 ga watan Disamba, 2022.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu ya laburta hakan a jawabin da ya fitar, wanda aka rarraba wa manema labarai a birnin tarayya Abuja.

Minista Isa Ali Pantami wanda ya aike da sakon a madadin shugaban kasa ya bayyana cewa Shehin Malamin ya fara samun sauki. Hakazalika ya ce Shehi ya godewa shugaban kasa bisa addu’ar samun lafiyar da yayi masa kuma yana masa addu’an nasara wajen gudanar da shugabancin kasar.

Labarai Makamanta