Rashin Iya Jagoranci Ne Ya Jefa Najeriya Halin Data Ke Ciki – Dr. Umar Arɗo

An bayyana cewar Najeriya ta fuskanci matsaloli da dama ta fuskar jagoranci na waɗanda ke rike da akalar ƙasar, wanda hakan shine babban dalilin da ya jefa ƙasar cikin halin ha’ula’i da ta tsinci kanta ciki tsawon lokaci.

Bayanin hakan ya fito ne daga bakin wani sanannen mai nazari da fashin baƙi akan siyasar Najeriya kuma kwararren masanin tarihi Dr. Umar Arɗo, a yayin tattaunawa da aka yi da shi a cikin shirin tambihi na gidan Talabijin din Liberty dake birnin tarayya Abuja.

Dr. Arɗo ya cigaba da cewar matsalar ƙasar ta samo asali ne daga gaza sauke nauyi da waɗanda nauyin kula da harkokin ƙasar ke kan kafaɗunsu, ɓangaren zaɓaɓɓun da naɗaɗɗu da kuma masu e zartar sha’anin mulki, inda kowane guda cikin wannan ɓangare ya gaza kai bantenshi abin da ya kaimu ga halin da muke ciki a yanzu.

Masanin tarihin ya kuma ɗora alhakin ƙara taɓarɓarewar al’amurra musanman a yankin Arewa ga waɗanda ya kira masu tsattsauran ra’ayi ta fuskar addini da kabilanci, wanda wannan ba ƙaramin illa ya yi wa yankin Arewa ba.

Dangane da yadda harkar tsaro a yankin Arewa ke ƙara fuskantar kalubale da koma baya, Dr.Umar Arɗo ya soki lamirin hukumomin hana fasa ƙauri a kasar da Hukumar shige da fice, inda ya bayyana rashin yin katabus din su a ayyukan su sun taimaka wajen jefa kasar cikin mawuyacin hali.
“Babu dalilin da zai sanya muggan makamai su yi yawa a hannun mutane, sannan baƙin haure suna sukuwa a cikin ƙasa muddin wadannan hukumomi suna gudanar da ayyukan su yadda ya dace”.

Dr.Arɗo ya kuma soki lamirin Sojoji bisa ga kutsen da suka yi akan sha’anin mulki a kasar, wanda wannan ya yi wa kasar illa da mayar da ita ajin baya, a tsakanin sauran ƙasashen duniya.

Akan batun da ake ta magana na yin sulhu ko kuma ɗaukar matakin buɗe wuta ga ‘yan Bindiga kuwa, masanin tarihin ya bayyana cewar harkar tsaro takan fara ne tun daga matakin gundumomi har zuwa jiha sannan tarayya, sannan a halin da tsarin Najeriya ke ciki yanzu Gwamnoni ba su da wani ƙarfi akan sarrafa jami’an tsaron dake Jihohin su sai dai su nemi alfarma, to tun da lamarin a harkar yake gyara zai yi wuya.

Labarai Makamanta