Rashin Iya Jagoranci Ne Silar Tabarbarewar Tsaro A Arewacin Najeriya – Ramalan

Shugaban Kamfanin ATAR Communications Mamallakan gidan Talabijin da Rediyon na Liberty Alhaji Dr Ahmed Tijjani Ramalan, a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, ya bayyana talauci a matsayin babban abin da ke haifar da rashin tsaro a yankin arewa maso yamma.

Ya bayyana cewa duk gwamnatin da ta gaza magance matsalar talauci da samar wa al’umma ci gaba a birane da karkara, to za ta fuskanci rashin tsaro da rashin zaman lafiya har illa masha Allah.

Tijjani Ramalan ya kara da cewa, babu tsammani mai kyau ga ‘yan Arewa a halin da ake ciki na tabarbarewar tsaro a shiyyar Arewa maso yamma, musamman ta la’akari da rashin hadin kai da gwamnonin yankin da dazukansu ke karkashin ikon ‘yan ta’adda.

Ya kara da cewa yadda al’amura suke a halin yanzu, tsarin lura da al’umma na gwamnatin tarayya da na jihohi ya ta’allaka ne a birane, yankunan karkara da kauyuka kuwa ba a damu da su ba. Shi ya sa suke fama da matsanancin talauci, wanda hakan ke haifar da ‘yan-ta’adda da masu garkuwa da mutane da mayar da al’amarin wata hanya ta kasuwanci.

Labarai Makamanta