Masarautar Bauchi ta tabbatar da tuɓe rawanin Alh muhammad Bello Kirfi a matsayin Wazirin Bauchi kuma dan majalisar masarautar Bauchi
A wata wasika mai dauke da kwanan watan 3 ga watan Janairu, mai dauke da sa hannun sakataren majalisar,
Alhaji Shehu Mudi Muhammad yace majalisar masarautar Bauchi ta ce gwamnatin jihar ta bada umarnin tsige Kirfi saboda rashin biyayya ga gwamna.
A takadar, mai lamba MLG/LG/S/72/T da kwanan wata 30 ga Disamba, 2022 ta ce, “abin da ke cikin wasikar ya nuna rashin biyayyar ka da rashin mutunta Gwamnan Jihar da gwamnati. Don haka ya ba da umarnin cire ka nan take.
“Saboda abubuwan da suka gabata, an cire ka daga mukamin Wazirin Bauchi da kuma ɗan majalisar masarautar Bauchi. Ina yi maka fatan alheri a duk abin da ka sa a gaba,” in ji wasiƙar.
Kafin zuwan wannan Gwamnatin dai an taba Dakatar da wazirin Bauchi wanda Hawan Gwamnatin aka mai da shi kan mukamin sa .
Kafin zuwa jiya kuma da aka tabbatar da cire shi kan kujeran sa kwata kwata.
You must log in to post a comment.