Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Rashin Albashi: Ma’aikata Sun Tsunduma Yajin Aiki A Jihar Filato

Labarin dake shigo mana daga Jos babban birnin Jihar Filato na bayyana cewar Ma’aikatan gwamnati a jihar sun shiga yajin aikin jan kunne na kwanaki biyar wanda ya fara a ranar Litinin, 12 ga watan Disamba Ma’aikata sun yanke shawarar daina aiki na wucin-gadi bayan gwamnatin ta ki biyansu albashi tsawon watanni uku.

Ma’aikatan sun kuma yanke shawarar tafiya yajin aiki saboda gazawar gwamnatin wajen sakin kudaden da ake ragewa kamar su kudaden fansho, garatuti da sauransu.

A wani taron manema labarai da ya gudana a Labour House da ke Jos, babban birnin jihar Filato a ranar Litinin, shugaban kungiyar JNPSNC, Titus Malau, ya ce sun yanke shawarar shiga yajin aiki bayan ya fito karara cewa gwamnnatin bata yin abun da ya dace don biyansu albashin da suke bi.

Hukuncin ma’aikatan na shiga yajin aiki na zuwa ne kwana daya bayan shugaban ma’aikatan jihar, Sunday Chong, ya yi alkawarin cewa gwamnati za ta biya su bashin albashin da suke bi.

Kungiyoyin kwadago sun aika wasika ga gwamnati kafin daukar wannan matakin A ranar Alhamis da ya gabata, suna gargadin cewa ma’aikata za su shiga yajin aiki idan ba a biya albashin da suke bi ba a ranar Litinin.

“Wannan ya zama dole duba da cewar gwamnatin ta gaza wajen cike bukatunmu kuma musamman yarjejeniyar da aka cimmawa a ranar 11 ga watan Nuwamban 2022, da sa bakin sakataren gwamnatin jihar.

“Bukatar JNPSNC sune kamar haka: Rashin biyan albashi na wata uku daga Satumban 2022 har zuwa yau; rashin sakin tsarin albashi; rashin sakin ragowar kudin fansho daga Agustan 2022 har zuwa yau da rashin sakin karin albashi na karin matsayi da karin kudi na shekara-shekara da sauransu.”

Kungiyar ta kuma soki rahoton farar takarda na kwamitin da Nde Gobak ke jagoranta kan kin karawa ma’aikatan da suka kai girma, Shugaban kungiyar kwadago na jihar Plateau, Eugene Manji ya ce: “Muna ta tsammanin za su cike yarjejeniyar a ranar ko kafin 14 ga watan Nuwamban 2022, sannan ya kamata a biya cikakken albashin watan Agusta sannan ya kamata a biya albashin Satumba/Oktoba kafin karshen Nuwamba amma ga shi muna a Disamba.

Exit mobile version