Rashin Aiki Ga Matasa Ne Silar Matsalar Tsaro A Najeriya – Sarkin Kano

An bayyana cewa babban dalilin da ya sanya sha’anin tsaro ke ƙara taɓarɓarewa a kasar nan musanman yankin Arewacin kasar ya biyo bayan rashin ayyukan yi gami da talauci dake addabar matasa a yankin.

Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya bayyana hakan a fadarshi dake birnin Kano, lokacin da yake jawabi a yayin bikin cikarshi shekara guda da hawa karagar Sarautar Kano mai dimbin tarihi.

Martaba Sarki Ado Bayero ya ce akwai babbar barazanar tsaro a Najeriya ganin yadda ake samun karuwar Matasa a kasar da ba su da aikin yi da yadda talauci ke taka mummunan rawa a tsakanin su.

Sarkin na Kano ya bayyana hakan ne a yayin wata hira da gidan Rediyon BBC Hausa yayi dashi a ranar Talata inda ya alakanta rashin sanar da matasa irin shirye-shiryen da gwamnatin ta tanadar musu ya sa da yawa daga cikin su ke zaune babu aikin yi.

Aminu Ado Bayero ya bayyana hakan ne yayin da yake cika shekara ɗaya akan gadon sarautarKano, bayan da gwamantin Kano ƙarkashin jagorancin Gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje ta sauke dan uwansa, Muhammad Sanusi II.

Sarkin ya kuma ce ya ce yana ƙoƙarin bin sahun iyayensa wajen hada kan gidan sarautar Kano da ake ganin ya rabu sakamakon tuɓe Sarki Sanusi na II.

Aminu Ado Bayero ya kasance ɗaya daga cikin ‘ya’yan Sarkin Kano marigayi Alhaji Ado Bayero wanda ya lashe sama da shekaru 50 yana Sarautar Kano, da yawan jama’a na ganin hawan Aminu Ado Sarautar Kano zai farfaɗo da darajar masarautar bayan shiga wani hali da tayi a baya, biyo bayan siyasar kano da ta shiga ciki.

Labarai Makamanta