Rashawa: EFCC Ta Tsare Kwamishinan Ganduje

Wani rahoton Daily Nigerian ya nuna cewa kwamishanan kananan hukumomi na jihar Kano, Murtala Garo, na amsa tambayoyi a hannun jami’an hukumar hana almundahana da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau EFCC.

A cewar rahoton, ana binciken kwamishanan ne bisa mallakan wasu manya dukiya a jihar Kano da birnin tarayya Abuja. Kakakin hukumar EFCC, Dele Oyewale ya tabbatar da hakan ga jaridar yayinda aka tambayeshi.

Amma ya ce gayyatan kwamishanan kawai aka yi ba garkameshi ba. Ya ce an gayyaceshi ne don bayani kan wasu abubuwa.

Majiya ta bayyana cewa hukumar yaki da rashawan jihar Kano ta gayyaci kwamishanan yayi bayani kan dukiyokokin da ya mallaka na gidaje, motoci, gidajen mai, da sauransu.

Labarai Makamanta