Rashawa Ce Silar Fitar Dani Daga Ofis – Magu

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Tsohon shugaban hukumar yaki da masu yi wa arzikin kasa ta’annati EFCC Ibrahim Magu ya ce babu hujjar fitar shi daga hukumar EFCC.

Magu ya bayyana hakan ne a yayin wani bikin bayar da lambar yabo da kungiyar daliban matan arewa ta shirya domin girmama shi a ranar Lahadi a Abuja.

“Ni ina daga cikin mutanen da rashawa ta yaka, amma ina farin ciki kan abubuwan da suke faruwa a yanzu gaskiya na bayyana ga ‘yan Najeriya,” in ji shi.

Ibrahim Magu wanda ya samu wakilcin ɗansa Mohammad-Saeed Ibrahim-Magu, ya yabawa kungiyar game da girmama shi da ta yi da wannan lambar yabo ta “cancanta” kuma yace yana cike da murnar karbar kyautar.

Da take nata bayanin kakakin kungiyar Aisha Nasir ta bayyana magu a matsayin wani mutum na daban, kuma jajurtacce, abin da ya sa ya cancanci kyautar kenan.

Labarai Makamanta