Sakamakon ranar da majalisar ɗinkin Duniya ta ware na ranar ‘yanci ta duniya, wata Ƙungiya mai rajin kare yaƙin mata dake Kaduna wadda a turance ake kira da suna “Back To School” ta gudanar da taro a Kaduna domin jan hankali da wayar da kan jama’a akan cin zarafin Mata.
Shugaban kungiyar Abdul Ahmad ya bayyana cewar dalilin shirya wannan taron nasu shi ne domin fadakarwar da wayar da kan jama’a musamman Mata domin sanin muhimmancin kansu da kuma kare kai daga dukkanin nau’ika na cin zarafi.
Ahmad ya ƙara da cewar Kungiyar tasu ta samu gagarumar nasara wajen sake mayar da mata makaranta domin samun gajiyar ilimi da sanin darajar da Allah ya yi musu, kuma Alhamdulillah an samu nasara.
Da yake tofa albarkacin bakinsa wani mai babban jigo a Ƙungiyar Jibirin Sule Zakirai ya ce halin da mata musamman ƙananan Mata suka tsinci kansu a ciki abin takaici ne duba da iri halin da suke fuskanta na cin zarafi daga wasu jama’a marasa tarbiyya.
A zantawar da aka yi da ita Hajiya Aisha Abdulmuminu wadda take shugabantar wata kungiya dake yaki da cin zarafin mata, ta bayyana takaicin ta dangane da yadda cin zarafin yara mata ke ƙaruwa a kusan kullum inda ta bayyana faɗi tashi da suke yi ta hanyar yaƙi da hakan da taimakon kwamishiniyar harkokin mata ta jihar Kaduna Hajiya Hafsat Baba.
A jawaban su daban daban Dakta Aminu daga hukumar kare hakkin ɗan Adam da Miss Felitia sun bukaci iyaye musamman Mata da fallasa asirin dukkanin wanda ya ci zarafin ‘Ya’yansu ba tare da wata fargaba ba inda suka yi alkawarin ba da tasu gudummuwar akai.
You must log in to post a comment.