Ranar Rediyo: Rediyo Na Taka Rawar Gani Tsakanin Al’umma – Lawal Daura

Daga Muhammad Sani Yusuf Nassarawa

Adaidai lokacin da Ake bikin Ranar Radiyo ta Duniya Jama’a da Dama na bayyana ra’ayoyin su game da amfani Radiyo a Tsakanin Al’umma.

Wani Mazaunin Daki Biyu Dake Jabi Abuja Engr. Lawal Halilu Daura ya bayyana irin Muhimmancin da Rediyo ke da shi a Tsakanin Al’umma.

yace Zuwan Rediyo Ba Karamin Nasara bace Domin Kuwa badon Rediyon ba akwai Labarai da Dama da baza a San da faruwarsa ba.

Ya Kuma Bada Misalai da Cewa Koda labari ne Mutum ya kawo idan Yana son ayadda da labarina Dolene Ya zama Shima daga Rediyo ya Samo shi.

Da yake magana akan Dalilan Dake Sanya jama’a yarda da Labaran da aka ji su a Rediyo yace hakan na faruwane Sakamakon Tantance wa da Kuma Tabbatar da Gaskiyar Labari Kafin A Watsa shi a Rediyo.

Daga Karshe yace Wannan Rana ce Mai Muhimmancin Wacce Bai Kamata a Manta da Muhimmancinta ba a Kowacce Shekara.

Labarai Makamanta