Ranar Mata: Ba Zamu Manta Cin Zarafin Mata Ba – Mustapha Khalifa

Wannan Rana ta 8 ga watan Maris Ita ce ranar ƴancin Mata ta Duniya wacce majalijsar ɗinkin Duniya ta ware domin a jaddada muhimmanci da kuma matsayi da Mata suke da shi a jagoranci.

Dan haka ma yasa aka yi wa wannan rana ta bana taken ‘Mata A Jagoranci’ saboda ɗimbin mahimmancin da suke da shi a rayuwar mu ta yau da kullum.

Shugaban Ƙungiyar Kare haƙƙin Bil’adama Da Taimakawa masara ƙarfi ta rigar yanci International Foundation For The Less Privileged, Mustapha Haruna Khalifa ne ya faɗi haka a lokacin zantawa da manema labarai a kaduna.

Ya ce wannan shekara ta 2021 ta zo mana da wani yanayi idan aka yi Duba da yadda ake tauye haƙƙin Mata a ɓangarori daban-daban na zamanta kewa musamman Fyaɗe.

Domin a bana kawai daga ranar 1 ga watan Janairun 2021 zuwa yau 8 ga watan Maris matsalolin cin zarafin ƴaƴa mata da suka zo gaban mu suna da yawan gaske ciki har da Mahaifin da yayi wa ɗiyar cikin sa fyaɗe, Inji shi.

Da kuma Mahaifin da ya ce kada ƴaƴan sa Mata su sake amsa sunan sa a ko’ina kuma in ya mutu basu da gadon sa wannan rashin tausayi da ƙin kimanta Mata yana daga cikin abubuwan da ba zai yiwu mu mance Da shi kuma mu zura musu Ido ba.

Dan haka ya zama Dole mu tashi mu yaƙi cin zarafin ƴaƴa Mata a lunguna da saƙo na duk inda muka samu kan mu wannan zai sa mu zama jakadu na kare haƙƙin Bil’adama a faɗin Duniya.

A ƙarshe muna kira ga Hukumomin tsaro da na Shari’a da su ba mu Haɗin kan da ya kamata wajen hukumta duk wani wanda aka samu da cin zarafin ƴaƴa Mata ta kowacce Hanya.

Sa Hannu:

Ameera Abdulƙadeer,
Communication & Information,
Rigar Yanci International.

Labarai Makamanta