Ranar Dimukuradiyya: Ku Mallaki Katin Zabe Domin Zabar ‘Yan Takara Na Kwarai – Ramalan

Shugaban Kamfanin ATAR Communication mamallakan gidajen Talabijin da Rediyo na Liberty Alhaji Ahmed Tijjani Ramalan, ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su tabbatar sun mallaki katin zaɓe domin samun nasarar zaɓar ‘yan takarar da suka dace a zaɓen dake tafe na 2023.

Ramalan ya yi wannan kiran ne a sakon murnar ranar dimukuradiyya ta bana 12 ga Watan Yunin Shekarar 2023.

Shugabàn Kamfanin na ATAR ya bayyana ranar Dimukuraɗiyya a matsayin wata rana mai muhimmanci a Najeriya sannan ya yi amfani da wannan dama wajen kira ga ‘yan Nijeriya waɗanda ba su mallaki katin zaɓe na din-din ba da su yi kokari mallakar katin domin ba su damar zaɓar ‘yan takarar da suka dace.

Tijjani Ramalan ya ƙara da cewar tuni gidajen Talabijin da Rediyo na Liberty ya samar da shirye-shirye na musamman ga ‘yan Najeriya domin sanin cigaban da ake samu a mulkin dimukuradiyya da wayar musu da kai akan muhimmancin mallakar katin zaɓe ta hanyar haɗin gwiwa tsakanin ‘yan siyasa da Jam’iyyu.

Daga karshe shugaban Kamfanin ya bukaci ‘yan Najeriya da dagewa wajen sanya ƙasa cikin addu’o’i domin samun zaman lafiya da cigaban ƙasa gaba daya.

Labarai Makamanta