Ranar Dimukuradiyya: Buhari Zai Yi Jawabi Kai Tsaye A Safiyar Yau

Rahotannin dake shigo mana daga babban birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zai yiwa yan Najeriya jawabi na musamman da misalin karfe 7 na safiyar yau Lahadi, 12 ga watan Yuni, 2022 ranar dimukuradiyya.

Ministan yaɗa Labarai da al’adu Alhaji Lai Mohammed, ya bayyana hakan yayin hirar da ya yi da manema labarai a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Lai Mohammed yace zai yi jawabin ne sakamakon murnar ranar dimokradiyya ta shekarar nan ta 2022 wadda Shugaban ya sauya daga 29 ga watan Mayu zuwa 12 ga watan Yuni a wani mataki na girmama marigayi Abiola, mutumin da ake ganin shi ya lashe zaben shugaban kasa da ya gudana a shekarar 1993.

Hadimin shugaban kasa kan gidajen rediyo da talabijin, Buhari Sallau, ya bayyana cewa misalin karfe 7 na safe Shugaba Buhari zai yiwa yan Najeriya jawabin.

Labarai Makamanta