Ramuwar Gayya: ‘Yan Banga Sun Kai Hari Rugar Fulani A Jihar Neja

Rahotanni daga Jihar Neja na bayyana cewar aƙalla mutum 9 ne suka rasa rayukansu a wani hari da aka kai rugar Fulani a ƙaramar hukumar Mashegu ta jihar Neja.

Harin wanda ake zargin yan Bijilanti daga ƙauyen Maza Kuka ne suka aiwatar, ya faru tsakanin ranar Lahadi zuwa Litinin. Hakazalika ana tsammanin na ɗaukar fansa ne kan abinda ya faru ranar 25 ga watan Oktoba a masallacin garin Maza-Kuka.

Ɗaya daga cikin waɗanda lamarin ya shafa, Shehu Mohammadu, yace: “Yan bijilanti sun shigo ƙauyen mu, suka ƙona gidajen mu, sannan suka gudu. Matar ƙanina da ɗan jaririnta sun rasa ransu.” “Sun kuma kashe wani ƙani na, da ɗansa ɗan shekara 3, sun dai kashe mun ‘yan uwana 7, kuma dole na gudu in ba haka ba nima da sun kashe ni.”

“Mun bar ƙauyen, yanzun ina rayuwa a wani wuri mai nisa, kuma ba zan koma ƙauyen ba, domin nima kashe ni za su yi.” Shaidan da lamarin ya faru a idonsa, Alhaji Muhammadu Marike, yace yanzun haka yana gudun hijira ne a wajen jihar Neja.

“Banda harin da suka kashe dagacin garin Adogon Malam da ɗan uwansa, sun sake dawo wa. Sa’ar dana ci shine ɗaya daga cikinsu ya sanni, shine yace a kyale ni.” “Sun tafi da mutum 8, har yanzun babu wanda yasan inda suke.

Kakakin yan sanda reshen jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, yace hukumarsu ta tura da ƙarin jami’an yan sanda domin kame masu hannu a harin. Ya kuma yi kira ga al’umma su taimaka wa jami’an tsaro da bayanan sirri domin tabbatar da doka ta yi aikinta akan waɗan da suka aikata wannan ɗanyen aiki.

Labarai Makamanta