Ramalan Zai Kaddamar Da Shirin ‘Yanci Ga Mata Da Yara

Shugaban Kamfanin ATAR Communication mamallakan Gidajen Talabijin da Rediyo na Liberty Alhaji Ahmed Tijjani Ramalan da haɗin gwiwar matan majalisar dinkin duniya zai kaddamar da wani shiri na ‘yanci ga Mata da yara.

Ramalan ya bayyana hakan ne a cikin wata takardar sanarwa da ya fitar ranar Laraba kuma aka rarraba ta ga manema labarai a birnin tarayya Abuja.

Kamar yadda ya bayyana shirin zai mayar da hankali ne wajen taimako da wayar da kan Mata da yara musanman masu karamin karfi, domin shiga a dama dasu a cikin harkokin siyasa musanman a lokacin da babban zabe na shekarar 2023 ke ƙara tunkarowa.

Shirin ya samu rijista kuma an tsara zai karade dukkanin shiyyoyin kasar gaba daya, domin amfanin al’umma baki daya.

Ya ƙara da cewar shirin zai taimaka gaya wajen samar da kyakkyawar gwamnati da inganta mulkin dimukaradiyya, kuma zai taka muhimmiyar rawa wajen ilmantar da Mata da Matasa kan muhimmancin kuri’ar su a yayin gudanar da zaben shekarar 2023.

Labarai Makamanta