Ramadan: Ku Taimakawa Mabuƙata – Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari a jiya ya yi maraba da fara azumin watan Ramadan wanda za a azumta na tsawon kwanaki 30 ko 29.

A cikin sakon da ya aike wa ‘yan kasar na Ramadan, Buhari ya roki Allah da ya karbi “sadaukarwar da muka yi ya kuma kara hadin kai, kaunar juna, zaman lafiya da ci gaban kasar.”

Buhari, a cewar wata sanarwa daga mai magana da yawunsa, Garba Shehu, ya bukaci musulmin kasar da su yi hakuri da juriya tare da yin watsi da muryoyin da ke neman raba kan al’umma.

Ya kuma bukaci dukkan ‘yan kasa da su nuna jin kai ga miliyoyin marasa karfi kuma su tuna da wadanda rikici ya raba su da gidajensu da sadaukarwa da addu’oi a cikin wannan muhimmin lokaci.

Labarai Makamanta