Raina Yana Baci Idan Naji Ana Zagin ‘Yan Fim – Umma Shehu


Fitacciyar Jaruma a Masana’antar shirya finafinan Hausa ta kannywwod ta bayyana cewar duk lokacin da ta ji a nan zagin ‘yan fim tan jin rashin dadi a zuciyarta.

Jaruma Umma Shehu wacce aka fi sani da Zuli a cikin shiri mai dogon zango na Gidan Badamasi ita ce ta bayyana Hakan a tattaunawar su da Dimokaradiyya, dangane da irin kallon da a ke yi wa ‘yan fim a cikin al’umma.

Zuli ta ce “Magana ta Allah ba na jin dadi sam idan na ji a na zagin, sai dai Kuma ba na yin fada da masu yin zagin, saboda bai kamata na yi fada da su ba, don su na fadar ra’ayin su ne.”

Haka kuma ta ce “ita harkar rayuwa ba ka isa ka sa wani ya so wani dole ba, don haka bai dace ba ana zagin ‘Yan fim, a na cewa ai halin su kaza ne. Wallahi ko da a ce haka halin na su ya ke, zan ce ba haka ba ne don haka ba na fada da masu zagin mu, sai dai in ba su shawara.

“in sun ji to, in ba su ji ba Sai na tashi na bar musu wajen. Ni dai na san sana’a na ke yi Kuma ina samun rufin asiri a cikin ta,” acewarta.

Daga karshe ta yi Kira ga abokan sana’ar ta da su rika gudun abubuwan da za a ringa fadar magana a kan su.

Labarai Makamanta