Rahoton ‘Yan Bindiga: Gwamnatin Buhari Ta Ci Trust TV Tarar Miliyan Biyar

Hukumar da ke sa ido kan kafafen watsa labarai ta ƙasa NBC, ta ci tarar gidan Talabijin na Trust naira miliyan biyar saboda labarin da suka wallafa kan hare-haren da ake kai wa a jihar Zamfara mai fama da rikici.

Wata sanarwa da kamfanin Media Trust ya fitar ya ce hukumar, a wata takarda dauke da sa hannun darakta janar dinta Balarabe Shehu Illela, ta ce ta ci tarar Trust TV ne “saboda ta watsa rahoto na musamman da ya saba ka’idojin wasu sassan ayoyin dokar hukumar.”

Sai dai kamfanin Media Trsut ya ce a “Yayin da muke ci gaba da nazari kan matakin hukumar da kuma duba zabukan da muke da su, muna sanar da cewa a matsayinmu na gidan talbijin, mun yi amannar cewa muna aiki ne domin al’umma ta hanyar karin haske kan batun garkuwa da mutane mai sarkakiya da kuma yadda yake shafar miliyoyin jama’ar kasarmu.”

Sanarwar ta kara da cewa rahoton ya bi salsalar zaman dar-dar a tsakanin al’umma da kuma abubuwan da suka sanya rikicin da ya sa wasu ke daukar makamai da ke jefa mutane cikin gagarumin halin kaka-na-ka-yi.

Labarai Makamanta