PRP Ta Fi APC Da PDP Tabbas – Jega

An tabbatar da cewa jam’iyyar talakawa ta PRP ita ce jam’iyya ɗaya tilo a Najeriya wadda ta rage wa jama’a su runguma domin kai su ga tudun mun tsira, ta la’akari da tabbas da jam’iyyar ke dashi, idan aka kwatanta ta da sauran manyan jam’iyyu kamar APC da PDP a ƙasar.

Shugaban jam’iyyar na kasa, Farfesa Attahiru Jega, wanda ya bayyana hakan a ranar Litinin, yayin taron musayar ra’ayi na jam’iyyar a Birnin Kebbi, jihar Kebbi, ya ce jam’iyyarsu za ta tafi da kowa ba irin siyasar uban gida da ake yi ba a sauran jam’iyyu.

Tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta na kasa, INEC, ya ce siyasar uban gida ta mamaye siyasar Nigeria kuma ta yi wa kasar illa.

Farfesa Jega ya ce bisa la’akari da yadda abubuwa ke tafiya a jam’iyyarsa da kuma yadda al’umma ke rungumar ta a sassan kasar, yana kyautata zaton jam’iyyar PRP za ta fi alheri ga yan Nijeriya.

A kan batun takarar 2023, Jega ya ce ba yanzu ne lokacin da za a yi wannan batun ba, inda ya ce idan an saka batun takara a gaba, za a manta da batun saita jam’iyyar kan alkibla mai kyau.

“Muna sake yi wa jam’iyyar tsari mai kyau ne domin hada kai da dukkan masu ruwa da tsaki, hakan yasa muka shirya wannan taron musayar ra’ayin ga masu ruwa da tsaki a jihar Kebbi.

“Muna aiki domin ganin mun gina jam’iyyar da za ta zama zabi ga ‘yan Nigeria gabanin 2023 a maimakon manyan jam’iyyu biyu masu rinjaye a kasar,” in ji shi.

Labarai Makamanta