PDP Za Ta Kwaci Mulki A 2023 – Atiku

Rahotanni daga birnin Yola na Jihar Adamawa na bayyana cewar tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya bayyana yaƙininsa cewa yan Najeriya zasu sake miƙa ragamar mulkin Najeriya ga jam’iyyar PDP a 2023.

Atiku ya roƙi yan siyasa su girmama dokokin zaɓen jam’iyya da kuma kundin tsarin mulkin ƙasa yayin gudanar da kowane irin zaɓe.

Tsohon mataimakin shugaban yana cewa matuƙar ana son ɗorewar demokaraɗiyya to sai an tabbatar da ingancin zaɓe. Yan Najeriya basu da wani zaɓi da ya wuce jam’iyyar PDP a zaben 2023.

Atiku ya yi wannan furucin ne yayin da yake jawabi jim kaɗan bayan ya kaɗa kuri’arsa a wurin taron zaɓen shugabannin PDP a matakin jiha a mazabarshi dake Jihar Adamawa.

“Idan kuka duba zaku ga yadda zaben ke tafiya cikin adalci kuma ba ɓoye-ɓoye a lokuta da dama muna zama ne mu amincewa juna a kowane mataki.”

Rahoto ya nuna cewa sama da wakilan PDP 2,614 daga ƙananan hukumomi 21 na jihar Adamawa ne suka kaɗa kuri’arsu a wurin zaɓen.

Gwamnan jihar, Ahmadu Fintiri, shima ya samu damar zuwa ya kaɗa kuri’arsa a wurin babban taron jam’iyyarsa ta PDP.

Labarai Makamanta