Jam’iyyar adawa ta PDP ta yi Alla-wadai da jifan da ake zargi an yiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari a jihar Kano ranar Litinin, 30 ga Junairu, 2023.
Shugaba Buhari ya kai ziyara ta musamman jihar Kano domin kaddamar da wasu manyan ayyuka da gwamnatin jihar ta kammala.
Jam’iyyar PDP ta bayyana cewa wannan duk laifin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ne. Ta ce Tinubu da Ganduje sun shirya cin mutuncin Buhari shi yasa aka yi kokarin hanashi ziyartar Kano tun daga farko.
Kakakin jam’iyyar PDP, Debo Ologunagba, ya bayyana hakan a jawabin kar-ta-kwana da ya fitar da daren Litinin inda yace: PDP na matukar Alla-wadai da harin da wasu batagari suka kaiwa shugaba Muhammadu Buhari a jihar Kano wanda dan takara Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya dau nauyi.”
“Jam’iyyarmu ta lura da cewa wannan na cikin kaidin da dan takaran APC ke shiryawa don nuna bacin ransa ga shugaban kasa, ya tayar da tarzoma a kasa, ya dakatar da aukuwar zaben 2023, sannan ya mayar da demokradiyarmu koma-baya; bayan lura ba zai iya samun nasara a zaben ba.”
“Ya kamata a lura cewa dan takaran shugaban kasa na APC ya dade yana fito-na-fito da shugaba Buhari tun lokacin da Buhari yayi kira ga yan Najeriya su zabi wanda suka ga dama a zaben 2023.”
You must log in to post a comment.