PDP Ta Roki Kotu Ta Haramta Gangamin APC

Jam’iyyar PDP ta shigar da kara a babbar kotun tarayya Abuja, ta bayyana shirin gudanar da taron APC a matsayin wanda ya sabawa kundin tsarin mulkin kasa.

A kara mai lamba FHC/ABJ/CS/389 2022, ta nemi kotu ta soke jam’iyyar APC a matsayin jam’iyyar siyasa bayan ta gaza cika sharuddan sashe na 222(a) da 223(b) da 225 na kafa jam’iyya.

Ta hannun lauyanta, Samuel Irabor, PDP ta sanya sunayen Hukumar INEC APC, Rijistar Amintattun Jam’iyyar APC da Kwamitin Tsare Tsare-tsare.

PDP ta bukaci kotun da ta bayyana duk wasu ayyukan kwamitin riko na Mala Buni har da babban taron na ranar asabar a matsayin haramtattu.

Labarai Makamanta

Leave a Reply