PDP Ta Kafa Kwamitin Nema Wa Atiku Mataimaki

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta kafa kwamitin da zai yi aikin nemo wa dan takararta na shugaban kasa, Atiku Abubakar, mataimaki.

Makwannin da suka wuce ne tsohon mataimakin shugaban kasar ya lashe zaben fid da gwani, a matsayin wanda zai yi wa PDP takara a babban zaben 2023.

Shugaban jam’iyyar Sanata Iyorchia Ayu ne ya kaddamar da kwamitin a hedikwatar jam’iyyar da ke Abuja ranar Talata.

Mataimakin Shugaban jam’iyyar shiyyar Arewaci Ambasada Umar Damagum ne zai jagoranci kwamitin, a daidai lokacin da hukumar zabe wato INEC ke dakon a mika mata sunayen ‘yan takarar shugaban kasa da mataimaki a kwanaki masu zuwa.

Masu sharhin siyasa na ganin Atiku Abubakar, wanda ya fito daga Arewacin kasar, zai dauko mataimaki ne daga Kudanci, la’akari da yadda fasalin Najeriya yake.

Labarai Makamanta

Leave a Reply