PDP Ta Gargaɗi Sabon Shugaban Hukumar EFCC

Babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta buƙaci sabon Shugaban hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa EFCC Abdulrasheed Bawa da ya kula sosai wajen dawo wa hukumar martabarta ta asali.

Jam’iyyar ta shawarci Bawa da ya kaucewa maimaita kuskuren da tsohon Shugaban Hukumar Ibrahim Magu ya yi ta hanyar gujewa shiga siyasa ko ba da damar amfani da hukumar domin musgunawa ko tauye ƴanci ko domin azurta kai kamar “yadda ya faru da shugabanta da ya gabata.”

A wani jawabi ta bakin kakin Jam’iyyar ta PDP, Kola Ologbondiyan, a rannar Asabar, ya bayyana cewa waɗancan abubuwa su ne suka lalata ƙwarewar hukumar EFFC da kuma jirkita ayyukanta da sa mutane yanke ƙauna da cewa za ta tabbatar da adalci da kuma tafi da ayyukan ta yadda ya kamata.

“Muna tuna wa sabon shugaban hukumar EFCC cewa PDP ce ta kafa wannan hukuma ta yaƙi da cin-hanci da rashawa, amma ba a matsayin wata hanya ta cin zali da firgita ƴan Najeriya da ba su ji ba su gani saboda dalilai na siyasa da kuma dalilai na ƙashin-kai.”

Sannan ya cigaba da cewa, “PDP ta lura cewa sabon shugaban ya samu horo daga ƙwararru a hukumar wanda hakan ya sa ƴan Najeriya sa ran zai yi amfani da horon da ya samu wajen gyara tsarin aiki da dawo da martabarta daidai da na ƙasashen ƙetare.”

“Har’ila yau, Jam’iyyarmu na kira ga shugaban na EFCC cewa, ta la’akari da shekarunsa da horansa, ya kamata ya nuna kyakkyawan misali ga ƴan baya wajen sakawa ƴan Najeriya saboda ƙarfin guiwar da suke da shi a kan sa.”

Labarai Makamanta

Leave a Reply