Pantami Zai Maka Jaridun Da Suka Alaƙanta Shi Da Ta’addanci Kotu

Ministan sadarwa da tattalin Arziki na Digital Sheikh Dakta Isa Ali Ibrahim Pantami, zai maka jaridun da suka wallafa rahotan da ke alakanta shi da ta’ddanci a Kotu.

Minista Pantami, ya mayar da martani ne bayan daya daga cikin jaridun wato NewsWireNGR ta fitar da wasikar neman afuwan kan labarin da ta fitar da ke cewa Amurka ta sanya sunan ministan a jeren ‘yan ta’adda.

Jaridar ta ce bayan kaddamar da bincike ta gano cewa labarin nata ba shi da tushe kuma bashi da alaka da Amurka don haka tana neman afuwan wanda ta batawa suna da sauran masu karanta labaranta.

Jaridar ta bayyana cewa ta dauko labarin ne daga Daily Independent wadda ita ta soma wallafa wannan labarin.

Labarin na ikirarin cewa “Minista Pantami a baya yana yaba wa Abu Musab Al-Zarqawi a matsayin babban shugaba, wanda ya shiga ƙungiyar Al-Qaeda bayan ya yi hijira zuwa Afghanistan bayan harin da aka kai a Amurka na ranar 11 ga watan Satumbar 2001”.

Batun dai ya ja hankali sosai tsakanin ‘yan kasar musamman a shafukan sada zumunta.

Ministan dai ya ce za a hadu a kotu domin sanin muhimmancin bincike a aikin jarida kafin wallafa kowanne irin labari.

Labarai Makamanta