Pantami Ya Zama Gwarzon Musulmin Najeriya A 2020

Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Sheikh Dakta Isa Ali Ibrahim Pantami, ya tashi a matsayin gwarzon musulmin Nijeriya na shekarar 2020.

Jaridar Muslim News ta musulmai, ta bayyana cewa Isa Ali Ibrahim Pantami ne ya lashe kyautar musulmin shekara saboda irin hidimar da ya ke yi.

Wannan jarida wanda ta ke wallafe-wallafe a game da sha’anin addinin musulunci, ta ce Ministan ya yi zarra wajen inganta tattalin Najeriya.

Bugu da kari, Isa Ali Ibrahim Pantami, ya na kokari wajen ilmantar da al’umma game da addinin musulunci kamar dai yadda ya saba yi tun ba yau ba.

Jaridar ta bada wannan sanarwa ne a wani jawabi da ta fitar a ranar Juma’a ta bakin wanda ya shriya wannan bikin kyauta, Mista Rasheed Abubakar.

Rasheed Abubakar ya yi wa bikin da taken #MNAwards, domin a karrama zakakuran da su ka ba musulunci gudumuwa a shekarar 2020, da ta gabata.

Bayan kasancewarsa babban masanin addinin musulunci, Isa Pantami ya yi har digirin Ph.D. a jami’ar Robert Gordon da ke Aberdeen, ta kasar Ingila.

Ministan tarayyar ya gaji Mai girma gwamnan jihar Borno, Farfesa Umara Babagana Zulum, wanda ya lashe wannan kyauta da aka bada a shekarar 2019.

Labarai Makamanta