Pantami Ya Zama Gwarzon Minista Na Shekarar 2021

Rahotanni daga babban birnin tarayya Abuja na nuna cewa Mai girma Ministan sadarwa da bunkasa tattalin arzikin zamani na kasa, Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami ya samu lambar yabo ta gwarzon Minista a shekarar 2021.

Isa Ali Ibrahim Pantami ya samu kyautar gwarzon Ministan Najeriya da ya yi fice da kwarewa ta fuskuki da dama a cikin shekarar nan. Kamar yadda rahotanni su ka tabbatar, mujallar nan ta People and Power ce ta ba Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamanin wannan lamba.

Ma’aikatar sadarwa da bunkasa tattalin arzikin zamani ta tabbatar da wannan kyauta da Ministan ya samu. Ma’aikatar tarayyar ta ce an zabi Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami, an ba shi wannan kyauta ne saboda irin tarin gudumuwar da manufofin ofishinsa su ka kawo.

Daga cikin abubuwan da su ka sa aka ba Ministan wannan lambar yabo da jinjina, akwai tsarin danganta lambar ‘dan kasa da layin wayar salula da ake yi. Bayan haka, mujallar People and Power ta yaba da manufofin sadarwa na zamani da Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami ya shigo da su bayan ya shiga gwamnati.

Ba wannan ne karon farko da Isa Pantami ya lashe irin wannan kyauta ba, an yi irin haka a baya. Mutane sun tofa albarkacin bakinsu game da wannan lambar yabo da aka ba Ministan, wasu suna ganin ya cancanci wannan karrama wa da aka yi masa. A daidai wannan lokaci kuma wasu sun soki lamarin, inda suka cigaba da yin kira ga Ministan ya ajiye mukamin da yake kai saboda zargin da ake jifansa da su.

Labarai Makamanta