Ministan Sadarwa da Tattalin arzikin zamani, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ya lashe lambar yabon kirkire-kirkire na ilmin zamani da gwamnatin tarayyar Najeriya tayi.
Shugaba Buhari ya gabatar masa da lambar yabon ne ranar Juma’a, 21 ga watan Oktoba, 2022 a taron karrama ma’aikatan gwamnati da suke nuna jajircewa. Taron ya gudana ne a fadar shugaban kasa dake Aso Rock Villa, Abuja.
A ranar Laraba, Shugaba Muhammadu Buhari ya taya Ministan Sadarwa da tattalin arzikin zamani, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, murnar cika shekaru hamsin cir a duniya. Buhari ya bayyana cewa Malam Pantami na daya daga cikin ma’aikata mafi kwazo, jajircewa da amfani a gwamnatinsa.
A jawabin da mai magana da yawun shugaban kasa Malam Garba Shehu ya fitar, Buhari yace zaben Pantami na daya daga cikin shawari mafi amfani da yayi a rayuwarsa.
You must log in to post a comment.