Pantami Ya Jinjinawa Budurwar Da Ta Ƙirƙiri Manhajar Hana Fyaɗe

Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani Dakta Isa Ali Ibrahim Pantami FNCS, FBCS, FIIM ya karrama Malama Sa’adat Aliyu Budurwar da ta kirƙiro da manhajar yaƙi da fyade a madadin Gwamnatin tarayya.

Dr. Isa Ali Ibrahim Pantami ya mika wa wannan Baiwar Allah takardar yabo saboda kokari na fasahar da ta yi kamar yadda aka sanar a shafin sada zumunta na Twitter.

Rahoton ya bayyana cewa Isa Ali Ibrahim Pantami ya ba Sa’adat Aliyu takarda ta musamman a ofishinsa da ke cikin ma’aikatar sadarwa da tattalin arzikin zamani a madadin Gwamnatin tarayya.

An dauki gajeren lokaci wajen bikin bada wannan wasika ga Malama Sa’adat Aliyu saboda aikin da ta yi.

Ministan tarayyar ya ce wannan budurwa ta yi kokari da ta kawo wannan manhaja a lokacin da ake fuskantar barazanar fyade da lalata da kananan yara.

Wadanda ake yi wa fyade su kan jin kunyar su kai kara saboda tsangwama a al’umma, don haka Ministan ya taya Sa’adat Aliyu murnar wannan fasaha da ta nuna.

Pantami ya yi kira ga gwamnati ta taimaka wa mata domin su cin ma burinsu a rayuwa.
Hakan na zuwa ne jim kadan bayan an samu labarin wannan manhaja.

A karshe Ministan ya yi kira ga hukumar NITDA ta hada kai da matasa masu taso wa domin a cigaba da kirkirar hanyoyin fasaha da za su taimakawa kasar irin wannan.

Labarai Makamanta