Pantami Bai Cancanci Zama Farfesa Ba – ASUU

Kungiyar malaman jami’a ta Abubakar Tafawa Balewa, wacce take a Jihar Bauchi ta bayyana cewa: ita sam, har yanzu bata gamsu da dacewar mukamin farfesancin da aka ba wa ministan sadarwa, Isah Phantami ba a jami’ar Federal University of Technology, Owerri, da ke Jihar Imo.

Shugaban ASUU da ke jami’ar Tafawa Balewa, Ibrahim Inuwa, a yayin da ya ke gabatar da jawabi wa manema labarai ya bayyana cewa;”Kungiyar malaman jami’ar ta nesanta kanta daga duk wani sakon taya murna da hukumar makarantar Tafawa Balewar ta aika wa Ministan”.

A nasa bangaren, ya bayyana cewa; mukamin farfesanci na Pantami zagaye take da cece-ku-ce kuma ta tayar da husuma a duk fadin kasar.

Labarai Makamanta