Osinbanjo Ya Yi Tir Da Kisan ‘Yan Arewa A Kudanci

Mataimakin Shugaban ƙasa Farfesa Yemi Osinbajo yayi tir gami da Allah wadai da kisa tare da harin da ake kaiwa yan Arewa a Kasuwar Shasha Ibadan.

Mataimakin Shugaban kasar ya siffanta hakan a matsayin dabbacin kuma abin kunya tsakanin Hausawa da Yarbawa, waɗanda aka san su a matsayin ‘yan uwa kuma abokanan zama shekaru da dama.

A cewarsa, kasuwar Sasha kasuwace da Hausawa ke rayuwa tare da Yarbawa tsawon shekaru, cikin zama na lumana da amana. “Babu shakka wannan abin da ya faru aikin Shaiɗan ne da ya kamata kowa yayi Allah wadai shi.

Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi lokacin da yake mayar martani dangane da arangamar da aka samu tsakanin Hausawa da Yarbawa, inda ya la’anci rikicin kabilancin yana mai bayyana shi a matsayin abin takaici,

Osinbajo ya ce shahararriyar kasuwar Shasha dake Ibadan Jihar Oyo alama ce ta hadin kai tsakanin Hausawa da Yarbawa wadanda suka daɗe suna kasuwanci da dama shekaru da dama.

Da yake magana a Legas lokacin da ya kai ziyarar ta’aziyya zuwa gidan marigayi Lateef Jakande da ke Ilupeju, mataimakin shugaban kasan ya ce: “Shekaru da dama, ‘yan kasuwa daga Arewa sun yi kasuwanci da ’yan uwansu daga Kudu maso Yamma kuma sun zauna lafiya har ma sun yi aure. Shasha wakiliyar hadin kai ne.”
Osinbajo yayi Allah wadai da rikicin Shasha.

Osinbajo ya yi gargadi game da bai wa rikicin sunan rikice-rikicen kabilanci, yana mai cewa: “Rashin jituwa da ke tasowa tsakanin mutane ko kuma idan wani laifi ya faru da wani a kan daya dole ne mu tabbatar mun gan shi yadda abin yake, a matsayin laifi, wanda dole ne a hukunta shi bisa doka.

Ba rikicin kabilanci ba. Osinbajo ya kuma gargadi daidaikun mutane game da daukar doka a hannunsu, yana mai cewa, “Kowane dan Najeriya yana da damar da kundin tsarin mulki ya ba shi na rayuwa, aiki da jin dadin rayuwarsa cikin aminci, zaman lafiya a karkashin doka.

“Hakkin gwamnati ne ta hanyar ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro su kame tare da gurfanar da duk wani mutum da ya aikata laifi kan wani dan kasar nan. Hakkin dan kasa ne ya taimakawa ‘yan sanda don gano masu laifin.

“Ina kira ga dukkan shugabannin al’umma da su yi aiki tare don kiyaye zaman lafiya da ‘yan uwantaka da mutanenmu daga sassa daban-daban na kasar da suke zaune a kasuwar Shasha tsawon shekaru da dama.”

Labarai Makamanta