Osinbajo Ya Ziyarci Dubai Kwana Biyu Da Dawowar Buhari

Rahotanni daga babban birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Mataimakin Shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya tashi daga Abuja inda ya nufi birnin Dubai, hadaddiyar daular Larabawa UAE rabar Litinin.

A cewar mai magana da yawun Osinbajo, Laolu Akande, mai gidansa ya tafi Dubai ne halartan taron kungiyar iskar Gas na girki. Ya bayyana hakane a jawabin da ya fitar ranar Litinin a birnin tarayya Abuja.

A cewarsa, Osinbajo zai gabatar da jawabi a wannan taro da za’a kwashe kusan mako guda ana yi kuma manyan Ministocin kasashen duniya zasu hallara.

Ya kara da cewa sama da mutum 2,000 daga kasashe 72 zasu halarci taron. Taron iskar gas WLPGA na gudana shekara bayan shekara tun da aka fara a birnin Amsterdam a shekarar 2019.

Jawabin ya kara da cewa mataimakin Shugaban kasan zai dawo Najeriya ranar Alhamis.

Labarai Makamanta