Osinbajo Da Tinubu Sun Gana A Abuja

Ana tsaka da rade-radin barakar da ke tsakanin Tinubu da Osinbajo kan batun takarar shugabancin kasa, sai gashi manyan ‘yan siyasar na kasar Yarbawa sun ci karo a birnin tarayya Abuja a ranar Juma’a, Dukkan ‘yan siyasan biyu sun bayyana farin cikin haduwa da juna inda cike da walwala suka rungume juna.

Kamar yadda ake yadawa, Osinbajo na hararo kujerar Buhari yayin da jagaban Tinubu ya ke hango hakan, inda ake rade radin cewa jigogin siyasar kasar Yarbawan ba sa ga Maciji da juna.

An ruwaito cewa, sun rungume juna cike da farin ciki yayin da ake ta rade-radin su biyun ba su ga maciji saboda kowa na son fitowa takarar shugabancin kasa a 2023.

Daga Tinubu har Osinbajo, babu wanda ya fito fili ya bayyana bukatarsa na son fitowa takarar, amma akwai alamun cewa dukkansu suna son maye gurbin Buhari.

Labarai Makamanta