Fadar Shugaban ƙasa ta mayar da kakkausan martani kan kalaman da Tsohon Shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya yi a saƙonsa na sabuwar shekara.
A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa Malam Garba Shehu ya fitar, sanarwar ta ce Obasanjo ba zai taɓa daina caccakar Shugaba Muhammadu Buhari ba sakamakon Obasanjon ba zai daina baƙin ciki kan duk wani wanda ya sha gabansa a ayyukan ci gaban ƙasa ba.
Fadar shugaban ƙasar ta buga misali da cewa Shugaba Buhari ya kammala gadar Neja ta biyu bayan an yi shekara 30 ana alƙawura a kanta.
Haka kuma fadar shugaban ƙasar ta ce Obasanjo ya yi wa kudu maso gabashin Najeriya ƙarya domin ya samu ƙuri’unsu, amma Shugaba Buhari bai samu ƙuri’unsu ba amma duk da haka sai da ya yi musu aikin gadar.
Fadar shugaban ƙasar ta kuma ce Obasanjo yana baƙin ciki ne sakamakon yana ganin yadda Buhari ke samun lambobin yabo da kuma yadda shugaban ke ci gaba da da’awar cewa zai tabbatar an gudanar da sahihin zaɓe fiye da wanda ya kawo sa kan karagar mulki.
You must log in to post a comment.