Obasanjo Da Gumi Sun Bukaci Gwamnati Ta Yi Wa ‘Yan Bindiga Afuwa

Tsohon shugaban kasa Chief Olusegun Obasanjo da Fitaccen Malamin addinin musulunci Sheik Ahmed Gumi sun nemi gwamnatin Buhari ta yi wa tubabbun ‘yan bingida afuwa, domin samar da kyakkyawan tsaro mai ɗorewa a ƙasar.

Wannan na zuwa ne bayan wata ziyara da Malamin addinin ya kai wa tsohon shugaban Najeriyan a gidansa da ke Abeokuta babban birnin jihar Ogun.

Obasanjo ya ce, “Yan bindigar da suka shirya fita daga daji da kuma daina muggan laifuka, a yi musu afuwa a gyara halayyarsu a koya musu ayyuka a basu jari ya zama suna da aikin yi”.

Wannan ne karon farko da aka ji Obasanjo na irin wadannan kalamai game da matsalar tsaro da ake ganin ta kusa mamaye yankuna da yawa a kasar.

Sai dai kuma ba wannan ne karon farko ba da Sheik Gumi ke neman a yi wa ‘yan bindigar ahuwa ba.

Hakazalika tsohon shugaban kasar da malamin addinin sun ba da shawarar kafa kotuna na musamman da za su yi shari’ar ’yan bindiga, masu satar mutane da masu safarar muggan makamai a Najeriya.

A wani bangaren sanarwar da suka fitar sunce; “Ya kamata Gwamnatin Tarayya ta dauki batun da muhimmanci a tsakanin ECOWAS don yin aiki a magance matsalar yan bindigar.

“Kowace al’umma dole ne a karfafa ta kuma a ba ta karfin gwiwa don tsayawa tsayin daka da karfi kan masu laifi.

“Ya kamata a samu kariya da tukuici a boye ga masu tsegunta masu laifi da ke rayuwa a cikin alumma. “Ya kamata a kirkiro kotuna na musamman don tunkarar shari’ar ‘yan bindiga, satar mutane, neman kudin fansa da kuma daukar makamai ba bisa ka’ida ba.

“Ya kamata taken ya zama: Tsaro nauyi ne da ke wuyan dukkan ‘yan Najeriya.

“Mun yarda da ci gaba da yin aiki tare don samar da mafita ga tsaron Najeriya da kuma neman wasu su kasance tare da mu kamar yadda muke yada bayanan hadin gwiwarmu a fili”

Labarai Makamanta