Obasanjo Da Atiku Duk Mayaudara Ne – Tinubu

Ɗan takarar shugabancin Najeriya a ƙarƙashin jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya shawarci al’ummar jihohin Kudu maso Gabas cewa kada su bi ra’ayin Obasanjo kuma kada su zaɓi Atiku a zaɓen shugaban ƙasa, domin mayaudara ne.

A ranar Laraba ce Tinubu ya bayyana haka a wurin kamfen a Enugu.

Tinubu ya gargaɗe su cewa su tuna irin yaudarar da Obasanjo da Atiku su ka yi masu a lokacin da su ke kan mulki.

Ya ce PDP a lokacin su ta yi alƙawurra da dama ga yankin, amma ba ta cika ba.

Ya buga misali da gadar Kogin Neja da ke Lokaja ta biyu, wadda mulkin Shugaba Muhammadu Buhari ya kammala kwanan nan.

Tinubu ya ce shi ma Atiku yaudarar yankin Kudu maso Gabas zai yi da ya ke cewa idan ya zama shugaban ƙasa ɗan ƙabilar Igbo ne zai gaje shi.

Asiwaju dai ya ragargaji Obasanjo ne saboda ya fito a fili cikin wata wasiƙar da ya fitar ya bayyana ra’ayin cewa Peter Obi na LP ne ya fi cancanta a zaɓa, ba Atiku ko Tinubu ba.

“Kada ku riƙa ɓata lokacin saurare da amincewa ga alƙawurran Obasanjo da Atiku. Su biyun duk mayaudara ne. Sun daɗe su na yaudarar ku tun daga 1999 har yau ba su daina ba,” cewar Tinubu.

Tinubu ya yi iƙirarin cewa Obasanjo da sauran shugabannin da su ka wuce na PDP sun kasa cika alƙawarin gina Gadar Kogin Neja, wadda ta haɗe Arewa da Kudu, amma sai yanzu mulkin APC ya kammala gadar.

Labarai Makamanta