Obasanjo Bai Harbu Da CORONA Ba- NCDC

Sakamakon gwajin cutar korona da aka yiwa tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya fito inda sakamakon ya bayyana baya dauke da cutar toshewar numfashin.

A wata takarda da Kehinde Akinyemi, mataimakin sa na musamman a fannin yada labarai ya fitar, ya ce an yi gwajin a ranar Juma’a, 7 ga watan Augustan 2020.

An yi gwajin ne a dakin karatu na Olusegun Obasanjo da ke gidansa na Pent House, Okemosan, Abeokuta, a babban birnin jihar Ogun.

Kamar yadda takardar da Akinyemi ya fitar a ranar Lahadi, 9 ga watan Augusta, ya ce Dr Olukunle Oluwasemowo ne ya dauki samfur din kuma yayi gwajin da ya dawo babu cutar a ranar Asabar.

“Dakin gwajin na daya daga cikin dakunan gwajin da hukumar yaki da cutuka masu yaduwa ta NCDC ta aminta da su don gwajin cutar korona,” takardar tace.

Labarai Makamanta