Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta karrama Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da lambar yabo gabanin taron Ƙungiyar Tarayyar Afirka da zai gudana a yau Juma’a.
Jim kaɗan bayan isarsa kasar ta Nijar, Shugaba Mohamed Bazoum ya karrama shi yayin wasu bukukuwa biyu da aka yi a ranar Alhamis.
Bayan ba shi lambar yabon, an saka wa wani titi a Yamai sunansa, sannan kuma aka ƙaddamar da wani littafi da aka fassara daga turancin Ingilishi zuwa na Faransanci game da mulkin Shugaba Buhari.
“Ina fatan wanna littafi zai zama alƙibla ga shugabannin Afirka masu zuwa kuma ya shata musu hanyar jajircewa da nagarta da kuma kishin ƙasa.
Shugabanin ƙasa da na gwamnatocin Afrika da dama ne suka suka isa Yamai babban birnin ƙasar don halartar taron na ƙungiyar African Union.
You must log in to post a comment.