Ni Ne Imam Mahadi – Mutumin Da Ya Yi Yunƙurin Kashe Limamin Ka’abah

Hukumomin da ke kula da Masallatai biyu Masu Daraja na Saudiyya wato Haramain Sharifain sun ce mutumin ya yi yunƙurin halaka Sheikh Bandar Baleelah ne lokacin da yake gabatar da huɗubar Sallar Juma’a.

Haramain Sharifain ta wallafa a shafinta na Facebook ranar Talata 25 ga watan Mayu cewa, mutumin wanda ɗan ƙasar Saudiyyan ne mai shekara 40, ya yi ikirarin cewa shi Imamu Mahdi ne.

Ya faɗi hakan ne a yayin da ƴan sanda suke tuhumarsa. Sai dai hukumar ba ta yi ƙarin bayani kan matakin da aka ɗauka a kansa ba.

Mutumin ya yi ƙoƙarin aikata wannan aika-aikar ne a yayin da yake sanye da harami a jikinsa.

Imamu Mahadi shi ne wani mutum da wasu Musulmai suka yi imanin cewa zai zo a ƙarshen duniya.

Haramain Sharifain ya wallafa bidiyon a shafukansa na sada zumunsa yadda mutumin ya yi yunƙurin kutsawa ga limamin da kuma yadda jami’an tsaro suka murƙushe shi.

Hukumomin sun ce “mutumin ya tunkari mumbarin limamin ne riƙe da makami a masallacin Ka’aba amma an yi nasarar murƙushe shi.”

Labarai Makamanta