Ni Ne Halastaccen Shugaban APC A Jihar Kano – Zago

Mutumin da ɓangaren Sanata Ibrahim Shekarau ya zaɓa a matsayin shugaban jam’iyyar APC a jihar Kano da ke Najeriya ya ce shi ne halattaccen shugaban jam’iyyar duk da kwamitin uwar jam’iyyar na sauraron korafin zaɓe ya fito fili ya ayyana Alhaji Abdullahi Abbas na ɓangaren gwamna Ganduje a matsayin shugaban jam`iyyar.

Alhaji Ahmadu Haruna Zago ya shaida wa BBC cewa babu abin da ya sha musu kai da aikin kwamitin sauraron korafin zaben, saboda zaben da suka yi sahihi ne.

Wannan iƙirarin dai ya ƙara fito da darewar jam`iyyar APC mai mulki a Kano, ɗaya daga cikin jihohin da ke da tasiri a siyasar Najeriya inda mutum biyu ke ikirarin kujerar shugabancin jam`iyyar a jihar.

Ɓangarorin biyu dukkaninsu sun gudanar da zaɓukan shugabancin jam’iyyar ne daban-daban.

Kuma ayyana Alhaji Abdullahi Abbas a matsayin shugaban APC a Kano da uwar kwamitin uwar jam’iyyar ya yi ya nuna cewa zaben ɓangaren su Haruna Zago akwai ƙila wa ƙala.

Amma Haruna Zago ya ce sun bi ka’idar zaɓen shugabancin APC kan tsarin yin maslaha ko zaben kai tsaye ko na deleget.

Kuma a cewarsa ana maslaha ga waɗanda suka sayi fom suka biya kudi a uwar jam’iyya, suka cike fom suka mayar – “su suke da haƙƙi a cikinsu su daidata.”

“A ƙa’idar jami’yyarmu a wajenmu ni ne shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano”, in ji shi.

Ya ƙara da cewa ya yi nasara ne ta hanyar masalaha tsakaninsa da abokan takararsa da suka sayi fom – mun sayi fom da ni da Sharu Baban Lungu da Nura Hassan kuma mun cimma maslaha a tsakaninmu, su biyun sun bar min, a cewar Ahmadu Zago.

Ya kuma yi iƙirarin cewa zaɓen da suka gudanar shi ne sahihin zaɓe, a cewarsa “cewa aka yi waɗanda suka yi zabe a rufe ba wanda suka yi zaben APC ba, ka ga ɓangarensu ne suka yi zaɓen rufe, mu kuma mu ne muka je muka yi sahihin zaɓe.

“Mu dama ba mu yi ƙorafi ba, zaben da aka yi ma wanda sauran suka yarda suka bar min kuma Turawan zaɓe suka bayyana a nan Kano ba wanda ya yi korafi. Saboda haka nasu ne suke da tangarda har suka yi korafi, alhali mu dama ba mu san wannan zaɓen nasu ba.”

Akwai yiwuwar sulhu?

Duk da cewa uwar jam’iyya ta nuna inda ta karkata amma ɓangaren Haruna Zago ya ce su ba su da masaniya, ba su ji matsayin jam’iyyar ba.

“Duk wani mutum da zai zo ya ce maka uwar jam’iyya ta fada to watakila bai san me ake kira uwar jam’iyya ba, mu ƴan siyasa ne mun san me ake nufi da hakan,” kamar yadda Haruna Zago ya yi iƙirari.

Ya jajirce cewa zaɓensa halastacce ne don zabi ne na mutum uku da aka yi maslaha.

Sai dai ya za su yarda da ƙofar sasanci yana mai cewa ba sabon abu ba ne samun ja’inja kan shugabancin jam’iyya a siyasance.

“Idan uwar jam’iya ta kawo mafita to dole duk mu hadu a tsari daya. Idan abu bai yuyuba ba to dole a cikinmu kowa ya san me ye matsayinsa a harkar siyasar” a cewar Zago, wata alama da ke nuna cewa akwai alamun ɓangaren zai iya ficewa jam’iyyar.

Labarai Makamanta