Ni Nayi Sanadin Matsalar Tsaro A Najeriya – Gwamna Wike

Gwamnan Jihar Ribas Nyesome Wike, yace a magana ta gaskiya shine ya yi sanadin taɓarbarewar tsaro dake addabar Najeriya wanda ke shirin tarwatsa zamantakewar ƙasar gaba daya, kuma ko kaɗan baya nadama akan abin da ya aikata.

Gwamna Wike ya ce ya jagoranci muguwar addu’ar ga Najeriya domin kasar ta fuskanci manyan matsaloli na ƙalubalen tsaro bayan da gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Buhari ta ki aike wa da jami’an tsaro jihar Ribas a lokacin da jihar ke fama da matsalar tsaro a 2016.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da ya ke jawabi wurin bude asibitin gidan gwamnati da ofisoshi a Birnin Fatakwal babban birnin jihar a ranar Alhamis.

Wike ya ce jihar Ribas ce kan gaba wajen yin garkuwa da mutane da wasu laifuka a lokacin da ya kama aiki amma da ya nemi taimako wurin Shugaba Muhammadu Buhari, zai aka yi zargin yana kashe ‘ya’yan jam’iyyar APC ne, bisa ga haka aka yi watsi da bukatar shi.

Don haka, sai ya yi addu’a Allah ya wanzar da rashin tsaro a sassar kasar har sai Shugaban kasa ya nemi afuwar jihar Rivers. “A 2016 da muka karbi gwamnati, akwai ƙalubalen rashin tsaro a jihar. Ina ta ihu. Na ruga wurin gwamnatin tarayya ‘ta bani dakaru na musamman kamar yadda na ji ana ba wasu.’ Suka ce ‘a’a. “Wai ina kashe ‘yan APC.

Sai na dawo gida na faɗa wa mutane na, ‘kowa ya koma gida ya yi addu’a, ya roki Allah wannan rashin tsaron ya cigaba da wanzuwa a Nijeriya har Nigeria ta rasa yadda za ta yi. “Kuma na fada musu ‘idan ba ku nemi afuwar jihar Rivers ba, ba za ka taba ganin zaman lafiya ba. Yanzu abinda ke faruwa a kasar nan kenan.

Domin sunyi fatan wannan jihar ta durkushe. “Gwamnoninsu da ke cewa muna kashe yan APC kuma yan PDP ne masu garkuwa, yanzu mene ke faruwa a Kaduna? Mene ke faruwa a Borno? Yau me ke faruwa a Ondo? Mene ke faruwa a sassan kasar?

Amma akwai zaman lafiya a Rivers. Ina ƙalubalantar su ce sun taimaka min ko da ta rana daya ne. Babu wanda ya yarda ya taimake ni. “A wannan jihar ne kawai gwamna ba zai iya zaben wanda zai zama kwamishinan yan sanda ba, tun 2015 zuwa yanzu mun samu kwamishinoni 15 na ‘yan sanda don ba su so Rivers ta cigaba.”

Labarai Makamanta