Ni Da Fim Mutu Ka Raba – Jaruma Hadiza Kabara


Masu kallon fina-finai masu dogon zango na Dadin Kowa da Gidan Badamasi ba za su kasa gane Hauwa matar Adahama ko Lantana ba, saboda irin rawar da take Takawa a cikin fina-finan.

To sai dai ba wannan ba ne fina-finan ta na farko, domin kuwa jaruma ce da ta ke cin lokaci biyu, sama da shekaru 20 da suka wuce.

Jaruma Hadiza Kabara ta yi tashen da babu wata jaruma da ta sha gaban ta, saboda yadda tauraruwar ta take haskawa a wancan lokacin. Bayan tsawon lokaci da aka daina ganin ta, sai kawai aka Jarumar ta fito a Gidan Badamasi da kuma Shirin Dadin Kowa.

Wannan ya sa wakilin Jaridar Dimukaradiyya ya ji ta bakin ta, dangane da dawowar ta bayan lokaci mai tsawo da ta shafe ba a ganin in da ta fara da cewar.

“To gaskiya harkar fim a wajena ba abu ne da za a ce na bar ta ba, domin tun da muka taso ita muka sani kuma ita muka iya don haka ba zan taba daina yin fim ba.

Ko da aka daina gani na tsawon lokaci na yi aure ne, shi ya sa, amma yanzu da aure na ya mutu sai na dawo harkar aka ci gaba da yi don fim sana’a ce a waje na. ”

Mun tambaye ta ko da ta dawo harkar a wanne yanayi ta same ta ganin duk babu sa’anin ta wadanda suka saba.

Sai ta ce” Gaskiya haka ne duk wadanda na samu a yanzu kanne na ne, amma dai duk in da mutum ya samu kan sa idan ya rike mutuncin sa to ba zai samu matsala ba, don haka muna zaune da su Lafiya suna ba ni girma a matsayina na yayar su, kuma babu wani abu da ya ke hada mu da su. ”

Mun tambaye ta bambancin harkar fim a tsakanin lokacin baya da kuma yanzu, sai ta ce

” To ai ka san komai na rayuwa ana samun sauyi, don haka an samu sauyi sosai a cikin harkar, don a baya jarumai sun fi yin suna kuma an fi yin zumunci sosai za ka ga kowa ya san kowa, sannan yawan fim din ma ba kamar yanzu ba, don a baya an fi yin finafinai da yawa, amma ka ga yanzu sai finafinai masu dogon zango, shi ya sa dole a samu bambanci sosai. Amma dai ina jin dadin fim din na yanzu sosai, ko don na dade ban yi ba ne ya sa hakan, don an fi biyan jarumai yanzu sosai a kan lokacin baya, kuma a yanzu abin ya fi tsari mai kyau kuma abin da ya fi ba ni mamaki, shi ne har yanzu mutane ba su manta da ni ba sun gane fuskanta, don ba boyayyiya ba ce, sai dai a ce na dan yi kiba, to sai ya zama da na dawo fim din sai na Kara karbuwa, farin jini na ya karu sosai a wajen mutane, don haka babu wani abu da zan ce sai dai na Kara godiya ga Allah da ya yi mini wannan baiwar. ”

Daga karshe Hadiza Kabara ta yi godiya ga dukkan masoyan ta da su ke tare da ita tun a shekarun baya da kuma wadanda suka karu a wannan lokacin.

Labarai Makamanta