Ni Ba Wakilin ‘Yan Bindiga Bane – Dr.Gumi

Mashahurin Malamin addinin Islama nan mazaunin garin Kaduna Sheikh Ahmad Abubakar Mahmoud Gumi ya fito fili ya fahimtar da jama’a matsayinshi na shiga tsakanin ‘yan Bindiga da gwamnati, inda ya fayyace cewa shi ba wakilin ‘yan Bindiga bane kamar yadda wasu jama’a ke bayyanawa.

Dr. Gumi ya faɗi haka ne ya yin da tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani ya kai masa ziyara a gidan shi dake Kaduna ranar Talata.

Shehu Sani ya kaima malamin ziyara ne domin tattauna batun akan ɗalibai 39 da aka sace a makarantar koyon zamanantar da gandun daji FCFM dake Afaka, jihar Kaduna da kuma mambobin ƙungiyar addinin kirista (RCCG) takwas da aka sace kwanan nan.

Dr Ahmad Gumi yace duk wasu shirye-shirye da yakamata ayi anyi don ganin an kuɓutar da ɗaliban waɗanda suka ɗauki tsawon makwanni biyu a hannun yan bindigan.

Ya ce akan lamarin ɗaliban mun yi duk abinda yakamata, har taro muka yi da iyayen ɗaliban kan suje su zauna da gwamnati.

“Na faɗawa iyayen ɗaliban inda matsalar take, sunje sun zauna da gwamnati sannan suka dawo wurina. Ni ba wakilin tattaunawa da yan bindiga bane.” “A duk tattaunawar da muka yi a baya muna tabbatar da akwai wakilan gwamnati tare da mu, kafin gwamnati ta bada umarnin harbe duk wanda aka gani ɗauke da bindiga.”Amma a kan ɗaliban kwalejin, muna iya bakin ƙoƙarin mu ta hanyar tuntuɓa muga ta yadda za’a warware matsalar.

Satin da ya gabata Sheikh Gumi ya shaidawa jaridar Dailytrust cewa umarnin harbi da gwamnati ta bayar ya dakatar da ƙoƙarinsa na kuɓutar da mutanen da aka sace.

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ba jami’an tsaro umarnin harbi ga duk wanda suka gani ɗauke da makami ba bisa ƙa’ida ba a cikin Daji.

Labarai Makamanta