Neman Lafiya: An Garzaya Da Uwargidan Shugaban Kasa Dubai

An garzaya da uwargidan shugaba Muhammadu Buhari, Hajiya Aisha Buhari, birnin Dubai, domin jinyan ciwon wuyan da take fama da shi tun bayan zuwanta Legas.

An samu labarin cewa uwargidan shugaba Muhammadu Buhari ta tafi Dubai ne tun washe garin Sallah sakamakon ciwon wuya da take fama dashi bayan komawa birnin tarayya Abuja daga jihar Legas.

Za ku tuna cewa a watan Yuli, Aisha Buhari ta kai ziyarar ta’aziyya ga Mrs Florence Ajimobi, uwargidan tsohon gwamnan Oyo, Abiloa Ajimobi, a gidansu dake Glover Road, Ikoyi, jihar Legas.

Ajimobi ya rasu ne ranar 25 ga Yuni sakamakon jinyan da yayi bayan kamuwa da cutar Coronavirus.

Yayin da ta koma Abuja, ta killace kanta na tsawon makonni biyu saboda ciwon wuyan da take fama da shi na kimanin wata daya bayan ta’aziyyar.

Abin ya tayar da hankalin na kusa da uwargidar kuma hakan ya sa aka garzaya da ita birnin Dubai don ganin Likita.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Uwargidan shugaban kasar yanzu haka tana hutawa a wani asibitin da aka sakaye sunansa amma tana cikin lafiya.

Labarai Makamanta