Neja: ‘Yan Bindiga Sun Harbe Mutum 16 Suna Cikin Sallah A Masallaci

Bala’in ya faru ne ana tsaka da gabatar da ibadar Sallar Asubahi da misalin ƙarfe biyar da rabi na subahi.

Sakataren Gwamnatin jihar Neja Malam Ahmad Matane, shine ya shelantawa manema labaru cewar bakin labarin ya faru ne da asubancin ranar Laraba a ƙauyen Baare dake ƙarƙashin karamar hukumar Mashegu.

Rahotan yace a take aka bindige mutane a kalla su 16 yayin da wasu da dama sun kareraye suna kwanciyar jinya.

Kamar yadda rahotan ya riske mu waɗanda ake zargin sun zo ne da asubahi ana Sallah kusan su 200 a kan mashina da muggan makamai.

Labarai Makamanta